Kamfanin dillancin labaran iqna, shugaba Hassan Rauhani ya ci gaba da cewa” Nauyi ne na addini da ya rataya a wuyan Iran ta kasance tare da al’ummar Yemen domin kalubalantar hare-haren da ake kai musu, haka nan kuma a lokacin da suke tattaunawar sulhu.
Shugaban Rauhani wanda ya gana da sabon jakadan kasar Yemen a Iran, Muhammad Muhammad al-Deilami ya jinjinawa tsayin dakar al’ummar Yemen wajen fuskantar wasu wuce gona da iri.
Dr. Hassan Rauhani ya kuma ce; Babu kokonto akan cewa a karshe tsayin dakar al’ummar Yemen zai kai ga samun nasara akan makiya.
A nashi gefen, sabon jakadan kasar ta Yemen a Iran Muhammad Muhammad al-Deilami ya ce; Kasarsa tana son bunkasa alakarta da Iran a fagage da dama. Har ila yau ya ce; Al’umar Yemen ba za su taba mancewa da irin taimakon da jamhuriyar musulunci ta Iran ta yi musu ba.”
Tun a cikin watan Ogusta ne dai kasar ta Yemen ta ayyana sabon jakadanta a Iran wanda ya mika takardun kama aikinsa ga ministan harkokin wajen Iran Muhammad Jawad Zarif a farkon watan Satumba.