IQNA

Majalisar Dinkin Duniya Ta Ce Gina Matsugunnan Yahudawa Baya Kan Doka

17:30 - November 20, 2019
Lambar Labari: 3484260
Majalisar dinkn duniya ta ce gina matsugunnan yahudawa ya saba wa kaida kuma tana goyon bayan kafa kasar Falastinu.

Kamfanin dillancin labaran IQNA, kimanin kuri'u dari da sattin da biyar na mambobin majalisar dinkin duniya ne suka goyi bayan kudurin, yayin da 5 kacal suka ki amincewa, sai kuma wasu 9 da suka kauracewa jefa kuri'ar, yayin taron kwamiti na uku na babban zauren majalisar.

Kuri'ar ta kasance tamkar martanin gaggawa ne na duniya kan kalaman da sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo yayi a ranar Litinin, cewa mamayar da yahudawan mamaya na Isra'ila ke yi a yankunan yammacin kogin Jordan bai saba dokokin kasa da kasa ba a mahagar Amurka.

Da yake maraba da matakin, Ministan harkokin wajen Falastinawan Riyad al-Maliki ya bukaci kasashen duniya su hada kai domin amincewa da 'yancin Falasdinawa na samun 'yancin gashin kai da kuma kawo karshen mamayar da Isra'ila ke yiwa yankunan Falastinawa ba bisa kaida ba.

 

 

3858233

 

captcha