IQNA

Azhar Ta Kafa Dalili Kan Wajbacin Hijabi Daga Kur’ani

13:11 - November 23, 2019
Lambar Labari: 3484267
Cibiyar Azahar ta kafa dalili kan wajacin hijabin musulunci da ayoyi na 31 daga surat Nur da kuma 59 daga surat Ahzab.

Kamfanin dillancin labaran IQNA ya bayar da rahoton cewa, shafin Al’ummah ya saka labarin cewa, babbar cibiyar addini ta Azahar ta kafa dalili kan wajacin hijabin musulunci da ayoyin kur’ani mai tsarki.

A cikin bayanin cibiyar Azha ta bayyana cewa, babu wani dalili da zai sanya a yi wani tawili kan wadannan ayoyi wadanda suka bayani kan wajabcin lullubi ga mata.

Bayanin ya yi ishara da aya ta 31 cikin surat Nur inda Allah yake cewa: “Kuma ka ce wa mũminai mãta su runtse daga gannansu, kuma su tsare farjõjinsu kuma kada su bayyana ƙawarsu fãce abin da ya bayyana daga gare ta, kuma su dõka da mayãfansu a kan wuyan rigunansu, kuma kada su nũna ƙawarsu fãce ga mazansu ko ubanninsu ko ubannin mazansu…”

Sai kuma a cikin surat Ahzab aya ta 59 inda yake cwa: “Yã kai Annabi! Ka ce wa mãtan aurenka da 'yã'yanka da mãtan mũminai su kusantar da ƙasã daga manyan tufãfin da ke a kansu. Wancan ya fi sauƙi ga a gane su dõmin kada a cũce su. Kuma Allah Yã kasance Mai gãfara, Mai Jin ƙai.”

A cikin dukkanin wadannan ayoyi za a faimci wajabci ne kan lullubi ga mata, inda aka kebance wasu daga cikin wadanda lullubi ga mata bai zama wajibi a gabansu.

Abin tuni dais hi ne, batun wajabta hijiabi ko ullubi ga mata musulmi a Masr ya jawo tayar da jijiyoyin wuya, inda wasu ke ganin ewa ayoyin da suke yin magana kan hijiabi ba suna nuni da wajabci ba ne, wanda hakan ne yasa Azhar ta fitar da wannan fatawa.

 

3858687

 

 

captcha