IQNA

Babu Gaskiya Kan Cewa Saudiyya Da UAE Suna Taimakon Sudan

19:09 - November 24, 2019
Lambar Labari: 3484270
Kwamitin kwararru kan siyasar Sudan ya zargi shugaban majasar zartarwar kasar da sharara karya.

Kamfanin dillacin labaran IQNA ya nakalto daga quds Al-arabi cewa, kwamitin kwararru kan siyasar Sudan ya zargi shugaban majasar zartarwar kasar da sharara karya inda ya bayyana cewa kasashen Saudiyya da hadaddiyar daular larabawa ne ke taimaka ma Sudan.

Bayanin kwamitin ya ce wannan babban abin kunya ne ga shugaban majalisar tafiyar da kasar Sudan na yanzu, domin kuwa abin da ya yi da’awa ba gaskiya ba ne.

Haka nan kuma bayanin ya ce dukkanin abin da wadannan kasashe biyu suka baiwa Sudan, sun bayar da shi ne ga hambararren shugaban kasara  matsayin cin hanci, domin ya aike da sojojin haya wadanda za su yi musu yaki a Yemen.

Abdulfattah Burhan ya bayyana cewa suna samun goyon baya da dauki daga gwamnatocin Saudiyya da kuma hadaddiyar daular larabawa, yana mai kara tabbatar da matsainsa na biyayya gare su da kuma neman taimako, abin da masana da ‘yan syasa a Sudan suke bayyana shi da abin kunya.

3859110

 

captcha