IQNA

Hizbullag Ba Ta Amince Da Shigar Shugular Amurka A Harkokin Lebanon ba

18:15 - November 26, 2019
Lambar Labari: 3484274
Hizbullah ta kasar Labnon ta nuna rashin amincewarta da sharudan da kasar Amurka ta gindaya na kafa sabuwar gwamnati a kasar.

Kamfanin dillancin labaran IQNA ya nakalto Shekh Na'im Kasim mataimakin sakataren na kungiyar Hizbullah ta kasar Labnon ya na fadar haka.

Sheikh Kasin ya kara da cewa dole ne sabuwar gwamnati da za a kafa a kasar ta dauki matakin gudanar da sauye-sauye domin yaki da fasadi a kasar, sannan kuma ta kasance mai 'yanci wacce ba za ta amince da katsalandan kasashen waje a harakokin siyasar kasar ba.

Shekh Na'im ya ce katsalandan da magabatan Amurka ke yi cikin harakokin siyasar kasar shi ya hana kafa sabuwar gwamnati a kasar. Amurkan na ci gaba da tuntubar 'yan siyasar kasar ta Labnon don cimma manufofinta a sabuwar gwamnatin da za’a kafa, wato wacce zata ware kungiyar Hizbullah.

A jiya litinin ce kwamitin tsaron majalisar dinkin duniya ya nuna damuwarsa kan yanayin harakokin tsaro dake wakana a kasar Labnon, inda ya bukaci a kafa sabuwar gwamnati cikin gaggawa a kasar.

 

3859571

 

 

 

captcha