Kamfanin dillancin labaran IQNA, kotun da ta ke shari’ar Jagoran Harkar Musulunci ta Nijeriya, Sheikh Ibrahim Zakaky a birnin Kaduna da ke Arewacin Najeriya, ta yanke hukuncin a kai sh tare da mai dakinsa Malama Zinatu zuwa gidan kurkuku maimakon hannun jami’an tsaro na DSS.
Tare da cewa shehun Malamin yana fama da rashin lafiya, duk da haka bata nuna damuwa akan hakan ba.
Bugu da kari kotun ta tsaida ranar 6 ga watan Febrairu na shekarar 2020 mai zuwa a matsayin lokacin sake zama domin ci gaba da shari’ar.