Kamfanin dillancin labaran IQNA ya nakalto daga mujallar midleast eye cewa, Abdullah Hamduk Firayi inistan Sudan ya bayyana cewa zai fitar da sojojin kasa daga kasar Yemen a yakin da suke yi a kasar.
Ya bayyana hakan ne yau a wajen taron majaisar Atlantic a birnin Washington, inda ya bayyana cewa kasarsa ta gaji wani yaki da Umar Albashir ya jefa kasar a Yemen.
Hamdu ya ce babu wani daily da zai sanya kasar Sudan ta shiga yaki da Yemen, domin kuwa ‘yan uwansu musulmi da larabawa ne kawai ae kashewa a wannan yaki, wanda hakan bai dace ba.
Tun a cikin sekara ta 2015 ce dai Umar Hassan Albashir ya shigar da sojojin Sudan cikin yakin da Saudiyya ta kaddamar kan al’ummar kasar, inda suke yin yaki a matsayin sojojin hayar Saudiyya.