IQNA

Matsayin Sarkin Morocco Kan Isra’ila Ya Samu Karbuwa

23:29 - December 07, 2019
Lambar Labari: 3484298
Bangaren kasa da kasa, sarkin kasar Moroco yaki amincewa da bukatar saktaren harakokin wajen Amurka.

Kamfanin dillancin labaran IQNA, a jiya alhamis ne saktaren harakokin wajen Amurka Mike Pampeo ya shiga birnin Rabat inda ya gana da Firai ministan kasar Sa'adu-ddin Usmany da babban daraktan dake kula da harakokin tsaron kasar Abdulatif Hamushi.

Rahoton ya ce saktaren harakokin wajen na Amurka ya bukaci ganawa da sarkin kasar ta Moroco Muhamad na shida amma har ya zuwa yanzu bai samu amsawa da fadar sarkin ba.sannan kuma babu wata liyafa da aka shiryawa saktaren harakokin wajen Amurka a daren jiya kamar yadda ake yi a baya.

Har ila yau duk da cewa a baya an shiga gudanar da taron manema labarai tsakanin ministan harakokin wajen kasar ta Maroco Naser Bourita da takwaransa na kasar Amurka Mike Pampeo, amma daga baya aka dage taron.

Wasu kafafen yada labarai sun habarta cewa saktaren harakokin wajen Amurka ya kai ziyara ne kasar ta Maroco da nufin mayar da alakar kasar da haramtacciyar kasar Isra'ila.

 

3862209

 

 

 

captcha