IQNA

Dan Takarar Shugabancin Kasa A Aljeriya Ya Yi Akawalin Ga Mahardata Kur’ani

23:37 - December 07, 2019
Lambar Labari: 3484300
Abdulkadir Bin Qarina dan takarar sugabancin kasa a Aljeriya ya yi alkawalin bayar da digiri ga mahardata kur’ani da hadisi.

Kamfanin dillancin labara IQNA, Abdulkadir Bin Qarina dan takarar sugabancin kasa a Aljeriya ya sha alwashin bayar da shedar digiri ga mahardata kur’ani da hadisi. A  kasar matukar ya lashe zabe.

Ya ci gaba da cewa mahardata kur’ani mai tsarki suna da masayi na musamman a cikin al’umma wanda ya kamata a san da haka, domin kuwa iliminsu ya cancanci digiri.

A kan haka ya ce wadadnda suka hardace kur’ani baki daya, da kuma wasu hadisai na littafin Mukhtasar Khalil daya daga cikin manyan littfan hadisi na mazhabar malikiyya, za su karbi takardar digiri.

Wannan matsaya ta dan takarar shugabancin kasar ta Aljeriya dai na ci gaba da daukar hankula a hanyoyin yada labarai na kafar sadarwa na zumunta.

 

 

3862161

 

 

captcha