IQNA

Makaho Da Hardace Kur’ani Da Tarjamarsa A Cikin Ingilishi Da Faransanci

17:14 - December 09, 2019
Lambar Labari: 3484305
Abdullah Ammar makaho ne dan masar da ya hardace kur’ani da tarjamarsa a cikin Ingilishi da Faransanci.

Kamfanin dillancin labaran IQNA, tashar Almihwar ta watsa wata hira da tayi da Abdullah Ammar wanda ke fama da larurar gani dan masar da ya hardace kur’ani da tarjamarsa a cikin Ingilishi da Faransanci a cikin kankanin lokaci.

Abdullah Ammar ya bayyana cewa, tun yana dan shekaru 8 da haihuwa a cikin watanni 3 da rabi ya hardace kur’ani mai tsarki bai dayansa.

Abdullah Ammar kuma ya hadace dukkanin tarjamar kur’ania  cikin harsunan turancin Ingilishi da Faransanci, kamar yadda uma ya iya karanta kur’ani da kira’oi goma da ake da su.

A tsakanin shekarun 2016 da 2018, ya lashe gasar kur’ani a wurare daban-daban a duniya, kuma ya samu kyatuka na ban girma daga shugaban kasar masar Abdulfattah Alsisi.

3862540

 

 

captcha