IQNA

Al’ummar Iraki Ba Su Yarda Da Shigar Shugular Kasashen Ketare Ba

22:45 - December 14, 2019
Lambar Labari: 3484318
Dubban jama’ar Iraki ne suka gudanar da jerin gwano a Bagadaza domin nuna rashin aminewa da katsaladan daga waje.

Kamfanin dillancin labaran IQNA, mutane da dama ne suka gudanar da gangami da jerin gwanoa  birnin Bagadaza na kasar raki, domin nuna rashin aminewa da katsaladan da kasashen waje suke yi a cikin harkokin kasar.

Wannan dai na zwa e sakamakon yadda wasu suke yin afani da jerin gwanon da ake yi ne kasar wajen tayar da hankali da kuma barnata dukiyoyin gwamnati da na jama’a, da nufin cutar kasar a siyasance.

A nasa bangaren shugaban gungun Hikma Sayyid Ammar Hakim ya bayyana cewa, a halin yanzu babu ko daya daga cikin makusantansa da suke da niyyar tsayawa takarar neman kujerar firayi ministan kasar.

Al’ummar Iraki na zargin wasu masu shiga cikin zanga-zangar da cewa an dauki nauyinsu n daga wasu kasashe domin kawai su kawo tashin hankali da yamutsi a kasar kamar dai yadda ake gani.

 

https://iqna.ir/fa/news/3863840

captcha