IQNA

Shugaban Ghana: Kada Musulmi Su Bari Masu Tsatsauran Ra’ayi Su Magana Da Yawunsu

13:28 - December 17, 2019
Lambar Labari: 3484324
Shugaban Ghana ya kirayi musulmi da kada su bar masu tsatsaran ra’ayi su rika yin magana da yawun musulunci.

Kamfanin dillancin labaran IQNA, shugaban kasar Ghana Nana Addo Dankwa Akufo-Addo ya kirayi musulmi da kada su bar masu tsatsaran ra’ayi su rika yin magana da yawun musulunci, musamman kungiyoyi irin su Daesh, Boko Haram, da alkaida.

Ya bayyana hakan ne a wurin taron mabiya darikar Tijjaniya na kasar Ghana, inda ya ce ko shakka babu addinin mulsunci bai koyar da tashin hankali da zubar da jinin jama’a ba gaira babu sabar ba.

A haka ya ce sun yi imanin cewa, kungiyoyin ‘yan ta’adda basa wakiltar sauran musulmi, kuma ya kamata musulmi su rika wayar da kan al’ummomi wajen nisanta kansu da addininsu daga masu bata musu suna.

Haka nan kuma yay aba da yadda musulm da mabiya addinin kirista suke zaune lafiya da juna a kasar Ghana, inda ya ce wannan abin alfahari ne kuma ain koyi ne ga dukkanin al’ummomi.

 

https://iqna.ir/fa/news/3864549

 

 

 

 

 

 

captcha