Kamfanin dillancin labaran IQNA, babban alkalin alkalan Afrika ta kudu ya ce suna ci gaba da bincike kan harin da aka kai wa masallacin Imam Hussain (AS) a garin Durban na kasar.
An bukaci mutumin da ake zargi wato Farhad Hummar da ya bayar da sautinsa domin bincike, domin kwatanta shi da sautin da aka dauka jim kadan bayan kai harin, wanda ya yi sanadiyyar rasuwa Muhammad Abbas Asup limamin masallacin.
Ana tsare da Hummar da wasu mutane 11 da ake zargin suna da hannua wannan harin, da ma wasu tuhumce-tuhumcen da suke alakanta su da ‘yan ta’adda.