IQNA

Taron ISESCO A Tunisia / Shawarar Iran Kan Tattaunawa Tsakanin Kasashen Musulmi

15:31 - December 18, 2019
Lambar Labari: 3484331
An bude babban taron raya ilimi da al’adu ta kasashen musulmi ISESCO a birnin Tunis na kasar Tunisia.

Kamfanin dillancin labaran IQNA, Abu Zar Ibrahimi Turkman shi ne shugabancibiyar yada aladun musulunci ta kasar Iran wanda ya wailci kasar a wurin taron, wanda kuma ya gabatar da irin shawarwarin da kasar ta Iran take da su a taron.

Ya ce kasarsa na da imanin cewa, farfado da tattaunawa tsakanin kasashen musulmi domin yin aike tare a dukkanin bangaroria  tsakaninsu, shi ne babban abin da zai kawo musu ci gaba.

Dangane da abubuwan da suke faruwa a halin yanzu da suka shafi musulmia  duniya kuwa, musamman ma yadda ake danganta musulunci da ta’addanci, ya bayyana cewa wannan babban zalunci ne ga addinin muslunci, addinin da ya shahara da zaman lafiya da yada kauna da tausayi da taimako a tsakanin bil adama.

Ya ce wata kila hakan ba zai rasa nasaba ba da yadda wasu daga cikin masu kiran kansu muuslmi suke aikata wasu abubuwa na jahilci da da rashin imani duk da sunan addinin muslunci, alhali addinin musulunci baya da alaka da abin da suke aikatawa.

Haka nan kuma ya bayyana cewa, daukar matakai na ilmantarwa na da matukar muhimmanci, domin hakan ne zai taimaka wajen nunar da matasa hakikanin koyarwa ta muslunci, wadda manzon Allah ya koyar da musulmi.

Ibrahimi Turkman ya ce duk wannan ba zai tabbata ba har sai idan gwamnatocin kasashen musulmi sun hada kansu sun yi aiki tare a wannan fage.   

 

3864921

 

captcha