IQNA

Saudiyya Ta Bayar Da Visa Hajji Da Umrah Miliyan 2.2

13:22 - December 23, 2019
Lambar Labari: 3484340
Mahukuntan Saudiyya sun sanar da bayar da visa mliyan 2.2 domin aikin hajji da Umrah.

Kamfanin dillancin labaran IQNA, ma’aikatar kula da harkokin aikin hajj da Umra ta sanar da bayar da visa ta Umar a cikin watanni hudu da suka gabata ga mutane miliyan daya da dubu 782, wasu miliyan daya da dubu 374 kuma sun yin Umra ne bayan hajji.

Daga kasar Pakistan mutane dubu 450, Indonesia dubu 399, sai kuma India mutane dubu 238 ne suka yi hajji da kuma umra da vida guda, yayin da Malaysia take biye mata da utane dubu 110, sai kuma masar da mutane dubu 85.

Bayan nan kuma isa wanann bayani sai kasar Turkiya da mutane dubu 70, Aljeriya uma mutane dubu 64, Bangaladesh dubu 61, hadaddiyar daular larabawa 37, sai kuma Jordan muane dubu 27.

A shekaar bana dai mahukuntan Saudiyya sun dauki matakan domin hana yaduwar bakin cututtuka a tsakanin masu aikin hajji da Umrah.

 

https://iqna.ir/fa/news/3865763

captcha