IQNA

An Bude Cibiyoyin Horo Na Hardar Kur’ani 69 A Masar

21:51 - December 27, 2019
Lambar Labari: 3484351
Bangaren kasa da kasa, an bude cibiyoyin hardar kur’ani 9 da makarantun kur’ani 370 a Masar.

Kamfanin dillancin labaran IQNA, ma’ikatar kula da harkokin addini ta kasar Masar ce ta bayar da wannan sanarwa a karshen wannan shekara ta 2019.

Bayanin ya ce dukkanin wannan aiki an gudanar ad shi ne a cikin 2019, kamar yadda makarantun kur’ani 370 sun shiga aiki, 18 daga ciki suna baya da horo ga masu wa’azi.

Haka nan kuma cibiyoyi 69 na bayar ad horo kan hardar kur’ani, da makarantu 127 wadada ake koyar da wasu ilmomin na addini, sai kuma wasu ajujuwa 1851 na yaki da jahilci kan addini.

A cikin watan azumin da ya gabata kuma an aike da makaranta 55 da kuma masu isar da sakon addini 42 zuwa kasashe, kamar yadda aka shirya gasar kur’ani a dukkanin sassan kasar wadda makaranta 16,200 suka halarta, wanda hakan yana cikin ayyukan ma’aikatar na 2019.

 

https://iqna.ir/fa/news/3866841

captcha