IQNA

Gasar Karatun Kur’ani Mai Tsarki Ta Najeria A Lagos

21:14 - December 28, 2019
Lambar Labari: 3484353
Bangaren kasa da kasa, an fara gudanar da gasar kur’ani ta kasa baki daya a Najeria da ke gudana a birnin Lagos.

Kamfanin dillancin labaran IQNA, an bude gasar kur’ani ta kasa baki daya a Najeria da ke gudana a birnin Lagos fadar kasuwancin kasar, an fara bude taron ne da karanta jawabin sarkin musulmi Alh Sa’adu Abubakar, wanda ya yi kira zuwa ga yin aiki da koyarwar kur’ani a cikin dukkanin lamurran rayuwar musulmi.

Shi ma a nasa bangaren gwamnan jihar Lagos wanda ya gabatar da nasa jawabin, ya bayyana cewa lokaci da musulmi za su nisanta kansu duk wasu baragurbi da ke amfani da sunan addinin musulunci addinin zaman lafiya wajen aikata ba daidai ba.

Haka nan kuma ya yi ishara da cewa, koyarwar addinin muslunci ita ce yada zaman lafia lafiya da kaunar juna da girmama dan adam da taimakonsa da jikansa, a duk lokacin da aka samu musulmi baya yin haka to baya bin hakikanin koyarwar musulunci.

Wannan gasa dai an kasa zuwa bangarori biyu na mata da kuma maza, kamar yadda ita ce ta talatin da hudu da ake gudanarwa, kuma za ta ci gaa har zuwa mako farko na shekarar 2020.

Daga kowace jiha a Najriya akalla mutane 10 ne ke halartar gasar, inda adadin masu halartar gasar ya kai mutane 600.

Kafin wannan lokacin dai ungiyoyin musulmi a Lagos sun yi kira zwa ga tara kudi Naira miliyan 290 domin daukar nauyin gudanar da wannan gasa ta kur’ani mai tsarki.

 

https://iqna.ir/fa/news/3866953

captcha