IQNA

Adel Abdulmahdi: Harin Amurka A Iraki Keta Alfarmar Al’ummar Kasar Ne

19:36 - December 31, 2019
Lambar Labari: 3484363
Firayi ministan kasar Iraki Adel Abdulmahdi ya caccaki Amurka sakamakon harin da ta kai a kasar.

Kamfanin dillancin labaran IQNA, a zaman da majalisar ministocin kasar Iraki ta gudanara  jiya, firayi ministan kasar ya yi tir da Allawadai da kakkausar murya dangane da harin da Amurka ta kai a kan dakarun Hashd sha’abi a kasar.

Adel Abdulmahdi ya ce Amurka ba ta da hurumin kaddamar da haria  cikin kasar Iraki ba tare da amincewar gwamnatin Iraki ba, kuma yarjejeniyar da ke tsakaninsu ita ce yaki da ‘yan ta’adda musamman IS.

Ya ce dakarun sa kai na Hashd dukkaninsu Irakawa ne da suka sadaukar da rayuwarsu wajen kare kasar Iraki, dubban daga cikinsu sun rasa rayukansu a kan wannan tafarki wajen yaki da ‘yan ta’addan daesh, saboda haka kai musu hari da Amurka ta yi yana a mtsayin kaiwa dukkanin al’ummar Iraki hari ne.

Amurka ta kai wa dakarun Hashd hari ne bisa hujjar cewa suna saun goyon bayan Iran, kuma hakan barazana ce ga manufofin Amurka a Iraki da ma yankin gabas ta tsakiya.

 

https://iqna.ir/fa/news/3867774

 

 

captcha