IQNA

Dakatar Da Watsa Shirye-Shiryen Tashoshi 10 A Tauraron Dan Adam A Sudan

19:39 - December 31, 2019
Lambar Labari: 3484364
Ma’aikatar yada al’adu da sadarwa ta Sudan ta dakatar da tashoshin talabijin 10 bisa hujjar rashin lasisi.

Kamfanin dillancin labaran IQNA, Faisal Muhammad Saleh ministan ma’aikatar al’adu da yada labarai na kasar Sudan ne ya bayar da wannan sanarwa, daga ciki kuwa har da tashar talabijin Tayyibah ta ‘yan salafiyyah.

Kamfanin watsa shirye-shirye na Andulus ne dai ya mallaki dukkanin wadannan tashoshi guda 10, kuma dukkanin tashoshin suna gudanar da ayyukansu ne ba tare da lasisi a hukumance ba.

Bayanin ya ce an dauki wannan matakin ne daidai da ayar dokar kafofin sadarwa ta 2019, wadda ta hana kamfanoni da daidaikun mutane mallakar tashoshin talabijin da radiyo sai dai gwamnati kawai, ko kuma da amincewarta.

Tun a cikin watan Yunin 2008 ne aka bude tashar Tayyibah a birnin Kahrtum a lokacin mulkin hambararrar gwamnati, inda ake zargin cewa tsohuwar gwamnatin ce take marawa tashar baya.

 

https://iqna.ir/fa/news/3867923

 

 

captcha