IQNA

Jagora: Za Mu Yi Tsayin Daka A Gaban Makiya

11:06 - January 02, 2020
Lambar Labari: 3484368
Jagoran juyi a Iran ya ce, basu da niyyar shiga yaki da wata kasa, amma a shirye suke su kare kansu.

Kamfanin dillancin labaran IQNA, Jagoran juyin juya halin musulinci na kasar Iran, Ayyatollah Sayyid Ali Khamenei, yayi tir da kakkausan lafazi da harin sama da Amurka ta kai kan dakarun sa kai na Kata'ib Hizbullah a kasar Iraki.

Ayyatollah Sayyid Ali Khamenei, ya ce Iran a shirye ta ke ta maida martini kan duk wata irin barazana ga kasarta, kuma a shirye ta ke ta yaki duk wani da zai kasance barazana ga hurimin Iran da ci gabanta da kuma al’ummarta.

Jagoran ya kara da cewa ba zamu jefa kasar ciki yaki ba, amma wannan sako ne ga duk wani mai bakar anniya ga kasar ta Iran.

A wani sakon a shafinsa na Twitter, Jagoran juyin juya halin musulinci na kasar Iran, ya bayyana cewa ‘’ gwamnatin Iran, da al’ummarta dama ni kai na, muna tir da kakkausan lazafi da harin na Amurka a Iraki

A ranar Lahadi data gabata ce, Amurka ta kai harin sama kan dakarun sa kai kan Kata'ib Hizbullah a kasar ta Iraki, inda mutane 25 suka rasa rayukansu, lamarin da Iran din ta ce ya sabawa dokokin kasa da kasa da kuam hurimin kasar ta Iraki.

Lamarin dai ya jayo wa Amurka fishin al’ummar kasar ta Iraki, wadanda a jiya Talata suka farmawa ofishin jakadancin Amurka na birnin Bagadaza inda sukayi kone kone da fashe fashe, wanda ya kai ga a kwashe jami’an diflomasiyyan Amurka daga ofishin.

Amurka dai ta zargi Iran da hannu a lamarin na mamaye ofishin jakadancinta a Irakin, batun da Iran din ta musanta, tana mai cewa duk tsuntsun da ya janyo ruwa, shi ruwa kan daka, saboda al’ummar yankin gabadaya sun jima da suka kosa da kin jinin Amurka, saboda laifukan data aikata a kasashen Iraki da Afganistan.

 

 

https://iqna.ir/fa/news/3868100

 

 

captcha