IQNA

Jagora Yayin Ganawa Da Sarkin Qatar: Amurka Ce Mubbabin Matsalolin Yankin

23:52 - January 12, 2020
Lambar Labari: 3484406
Ayatollah Khamenei yayin zanatawa da sarkin Qatar a daren yau Lahadi, ya sheda cewa; Amurka e take jawo dukkanin matsaloli a gabas ta tsakiya.

Kamfanin dillancin labaran IQNA, Jagoran juyin juya halin musulinci na Iran, Ayatollah Sayyid Ali Khamenei, ya gana da sarkin Qatar Shaikh Tamim ben Hamad Al-Thani wanda ya ziyarci kasar ta Iran a wannan Lahadin.

Yayin ganawar, Ayatollah Sayyid Ali Khamenei, ya bayyana cewa duk Amurka ce da kawayenta umul’aba’isin halin da ake cikin a yankin nan, inda ya bukaci dukkan kasashen yankin su hada kansu domin kawo karshen kaka-gidan da Amurka ta yi a yankin.

A wani bangare kuma kuma, jagoran ya bayyana kyakyawar alakar dake tsakanin Iran da Qatar, sannan ya yi fatan kasashen biyu zasu ci gaba da kasancewa bisa irin wannan turba a fagage da dama.

A jiya Lahadi ne sarkin Qatar, Shaikh Tamim ben Hamad Al-Thani, ya fara wata ziyara aiki a nan birnin Tehran.

Yayin ziyarar tasa, sarkin na Qatar, ya kuma gana da shugaban kasar ta Iran, Dakta Hassan Rohani, baya ga wasu manyan jami’an kasar ta Iran.

Bangarorin sun tattauna kan batutuwa da dama da suka shafi alakar dake tsakaninsu dama yankin baki daya.

Wannan ita ce ziyara irinta ta farko ta sarkin na Qatar a Iran, tun bayan hawansa sarauta a shekara 2013.

Ziyarar ta sarkin Qatar na zuwa ne kwanaki kadan bayan kisan da Amurka ta yi wa babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin musulinci na kasar Janar Shahid Qasim Sulamaini, a Iraki, wanda kuma Iran din ta mayar da martani ta hanyar kai hare haren makamai masu linzami kan sansanonin sojin Amurka a Iraki.

 

 

https://iqna.ir/fa/news/3871109

captcha