IQNA

Trump: Sai An Biya Amurka Kudi Za Ta Fice Daga Iraki

0:00 - January 13, 2020
Lambar Labari: 3484408
Shugaban Amurka Donald Trump ya ce sai an biya su kudi kafin su fitar da sojojinsu daga kasar Iraki.

Kamfanin dillancin labaran IQNA, Shugaban kasar Amurka ya kara jadda cewa matukar gwamnatin kasar Iraki tana son Amurka ta fidda sojojinta daga kasar, to dole ne ta biya Amurka kudaden da take wajen ayyukan tsaro a kasar.

Shafin tashar talabijin ta Al-hurrah ta bayar da rahoton cewa; a zantawar da ya yi da tashar Fox News, Donald Trump ya jaddada cewa, babu batun ficewar sojojin Amurka daga Iraki, matukar dai ba a biya Amurka kudaden da ta kashe a kasar ba.

Trump ya ce matakin da ta dauka na kashe Kasim Sulaimani, mataki ne na tsaro, domin kauce wa abin da ya faru da jakadan Amurka a Benghazi Libya, ya sake faruwa da jakadan Amurka a Iraki.

Tun bayan harin da Amurka ta kai kan dakarun Hashd Sha’abi ne, al-ummar kasar Iraki ta kai farmaki kan ofishin jakadancin Amurka a Bagadaza, tare da kona wani bangaren na ofishin, lamarin da ya jawo dakatar da ayyuka a ofishin.

A daren Juma’ar makon da ya gabata ne dai Amurka ta kai wani hari, wanda ya yi sanadiyyar yin shahadar janar Kasim Sulaimani, da kuma mataimakin babban kwamandan dakarun Hash Sha’abi Abu Mahdi Almuhandis tare da wasu da suke rakiyarsu su 8. Bayan harin ne majalisar dokokin Iraki ta bukaci Amurka ta kwashe dukkanin dakarunta daga kasar Iraki.

 

 

https://iqna.ir/fa/news/3870740

captcha