IQNA

Jagora: Martanin Iran Kan Sansanin Sojojin Amurka Ya Zubar Da Haibar Amurka A Duniya

18:32 - January 17, 2020
Lambar Labari: 3484422
Bangaren siyasa, Ayatollah Khamenei ya bayyana harin mayar da martani da Iran ta mayar wa Amurka ya zubar da haibar Amurka a duniya.

Kamfanin dillancin labaran IQNA, jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana cewar harin da dakarun kare juyin juya halin Musulunci na kasar Iran IRGC suka kai sansanin sojojin Amurka a Iraki a matsayin mayar da martani da kisan gillan da suka yi wa Janar Qasim Sulaimani ya zubar da martabar Amurka wanda ba za ta iya dawo da shi ba.

Jagoran ya bayyana hakan ne a yayin da yake gabatar da hudubar sallar Juma’a a yau din nan a nan birnin Tehran inda yayin da ya ke magana kan shahadar Janar Qasim Sulaimani, ya jinjina wa al’ummar Iran sakamakon irin gagarumar jana’izar da suka yi wa shahidan, kamar yadda kuma ya jinjina wa dakarun IRGC din sakamakon martanin da suka mayar ta hanyar harba makamai masu linzami zuwa ga sansanonin sojin Amurka a Iraki, yana mai bayyana wadannan lamurra guda biyu a matsayin ranaku na Ubangiji da wajibi ne a gode wa Allah.

Jagoran ya bayyana cewa kisan gillan da Amurka ta yi wa Qasim Sulaimani ya zubar da mutumcin Amurkan da tabbatar da karyarta ta fada da ta’addanci don kuwa Qasim Sulaimani shi ne jagoran fada da ‘yan ta’addan kungiyoyin Daesh da sauransu.

A wani bangaren na jawabin nasa, Imam Khamenei ya nuna damuwarsa dangane da batun harbo jirgin saman fasinjan kasar Ukraine bisa kuskure da aka yi a Iran yana mai isar da sakon ta’aziyyarsa ga iyalan mutanen da abin ya shafa.

Jagoran ya bayyana cewar makiyan al’ummar Iran sun yi kokarin amfani da wannan damar wajen dushe hasken nasarar da al’ummar Iran suka samu sakamakon mayar da martani ga Amurka, to sai dai ya ce ko da wasa ba za su yi nasara ba.

A wani bangare na jawabin nasa, Jagoran yayi watsi da ikirarin kasashen turai uku, wato Birtaniyya, Faransa da Jamus na kai karar Iran kwamitin tsaron MDD kan ta karya yarjejeniyar nukiliya yana mai cewa Amurka ma ta gaza wajen dunkufar da al’ummar Iran ballanta su.

Tun kimanin shekaru takawas da suka gabata jagoran bai jagoranci sallar juma'a ba, amma a yau shi ne da kansa ya jagoranci sallar, sakamakon abubuwan ad suka faru a cikin makonni biyu a kasar.

Jawabin an jagora dai ya dauki hankulan kafofin yada labarai an duniya, inda suke ci gaba da nakalto kalaman nasa tare da yin sharhia  aknsu daidai da mahangarsu da kuma masana da suke zantawa da su.

 

 

 

 

https://iqna.ir/fa/news/3872175

 

 

 

captcha