IQNA

Shugaba Rauhani: Iran Ta Ci Gaba Da Tace Uranium Ba tare Da Kaidi Ba

18:42 - January 17, 2020
Lambar Labari: 3484423
Bangaren siyasa, shugaba Rauhani ya ce Iran ta ci gaba da tace sanadarin uranium ba tare da kaiba.

Kamfanin dillancin labaran IQNA, shugaban kasar Iran Dakta Hasan Rouhani ya bayyana cewar a halin yanzu babu wani shamaki a kan Iran dangane da shirin ta na nukiliya na zaman lafiya yana mai cewa a halin yanzu Iran tana tace sinadarin uranium sama da yadda ta kasance tana yi kafin yarjejeniyar nuliya ta shekara ta dubu biyu da sha biyar.

Rouhani ya bayyana hakan ne a wani jawabin da yayi wajen taron manyan jami’an babban bankin kasar ta Iran inda ya ce a halin yanzu dai babu wani abin da zai hana Iran ci gaba da aikinta na nukiliya na zaman lafiya, yana mai cewa matukar dai kasashen Turai suka ci gaba da yin watsi da alkawarin da suka dauka to Iran ma za ta ci gaba da rage wadannan alkawurra.

Haka nan kuma shugaba Rouhani ya ce Iran ta ci gaba da hakuri da kuma ci gaba da girmama yarjejeniyar nukiliya duk kuwa da shugaban Amurka Donald Trump ya fitar da kasarsa daga cikin yarjejeniyar wanda hakan yin karen tsaye ne ga yarjejeniyar.

Har ila yau shugaba Rouhani yayi kakkausar suka ga kokarin da shugaban Amurkan yake yi na tursasa sauran kasashen Turan da su fice daga yarjejeniyar.

A kwanakin baya ne dai Iran ta sanar da fara aiwatar da kashi na biyar na rage irin aikin da take yi da yarjejeniyar nukiliyan bayan da kasashen turai da suke cikin yarjejeniyar wato Birtaniyya, Faransa da Jamus sun gagara cika alkawurran da suka yi cikin yarjejeniyar ta nukilya da aka cimmawa tare da Iran.

 

https://iqna.ir/fa/news/3872062

 

 

 

captcha