IQNA

An Cafke Mutumin Da Ya kona Kur’an A Tunisia

22:02 - January 20, 2020
Lambar Labari: 3484435
Bangaren kasa da kasa, jami’an tsaru sun cafke mutumin da ya kona kur’ani mai tsarki a kasar Tunisia.

Kamfanin dillancin labaran IQNA, shafin yada labarai na khbrpress ya bayar da rahoton cewa, a jiya an kame mutumin da ya kona kwafin kur’anai a masallacin garin basbita da ke cikin gundumar Qasrain.

Mutumin mai shekaru 33 da haihuwa a duniya, ya fito daga gidan kaso ba da jimawa ba bisa zarginsa da aikata wasu laifuka, ida uma ya sake tafka wani laifin na kone kur’ani mai tsarki.

Bayan gudanar da bincike a gidansa, an gano wasu kwafin kur’ani da yak eta, kamar yadda kuma ya amsa cewa shi ne ya kona kur’anai a masallacin Basbita  akwanakin baya.

 

https://iqna.ir/fa/news/3872928

captcha