IQNA

Al’ummar Iraki Sun Gudanar Da Zanga-Zangar Neman Ficewar Amurka Daga Kasarsu

23:37 - January 24, 2020
Lambar Labari: 3484444
A birnin Baghdad Miliyoyin al’umma ne suka fito domin yin tir da kasantuwar sojojin Amurka a kasar Iraki, tare da yin kira da su gaggauta ficewa.

Kamfanin dillancin labaran IQNA, shafin yada labaran Iraki na almaalumah ya ambaci cewa; Tun da safiyar yau juma’a ne Irakawa da su ka fito daga dukkanin bangarorin al’ummar kasar suka fara cincirino domin yin gangamin a birnin Bagadaza da sauran birane.

Haka nan kuma masu Zanga-zangar suna dauke da kyallaye da aka yi rubutu akansu na bayyana Amurka a matsayin mabarnaciya, tare da yin kira a gare ta da ta janye sojojinta daga cikin kasar ta Iraki.

Rahotanni sun ambaci cewa An kafa wuraren bincike a sassa daban-daban na babban birnin kasar Irakin Bagadaza akan hanyoyin da su ke zuwa jadriyah da nan ne cibiyar gangamin inda miliyoyin mutane suka cika wuraren makil.

Wannan gangami dai yana gudana ne dai bisa gayyatar da Sayyid Muqtada Sadr ya yi wa Irakawa da su fito domin yin Zanga-zanga ta miliyoyin mutane cikin ruwan sanyi domin neman Amurka ta fice daga cikin kasar baki daya.

Tun a ranar biyar ga watan Janairu nan da ake ciki ne dai majalisar dokokin kasar ta Iraki ta fitar da kuduri na yin kira ga Amurka da ta tattara ya nata, ya nata ta bar kasar.

Kiran ya biyo bayan kisan gilla na ta’addanci da Amurka ta yi wa Janar Kassim Sulaimani na Iran ne, da kuma Injiniya Abu Mahadi al-Muhandis na rundunar sa kai ta Hashdu sha’abi wacce ta murkushe ‘yan ta’addan da suka addabi kasar ta Iraki.

 

 

https://iqna.ir/fa/news/3873770

 

 

 

captcha