IQNA

Kungiyar Kasashen Musulmi Za Ta Gudanar Da Zama Kan Yarjejeniyar Karni

23:57 - January 31, 2020
Lambar Labari: 3484468
Kungiyar kasashen musulmi ta sanar da cewa za ta gudanar da zaman gaggawa kan batun abin da ake kira yarjejeniyar karni.

Kamfanin dillancin labaran IQNA ya nakalto daga shafin Arab Alyaum cewa, kungiyar kasashen musulmi ta bayyana cewa, manufar zaman dai ita ce yin dubi kan wannan batu da kuma yin gyara a kansa.

Kungiyar ta jaddada cewa duk wani shirin kawo sulhu tsakanin falastinawa da Isra’ila dole ne ya zama kan ka’idoji da dokoki na kasa da kasa, da kuma kudirin kwamitin tsaron majalisar dinkin duniya.

Yusuf Bin Ahmad Alusaimin babban sakataren kungiyar ya bayyana cewa, birnin Quds bangare ne na falastinu, wanda ba za a iya raba shi da Falastinu a cikin iyakokinta na shekara ta 1967 ba.

Baya ga zaman da kungiyar kasashen musulmi za ta gudanar a ranar Litinin mai zuwa, a yau Asabar ma kungiyar kasashen larabawa za ta gudanar da nata zaman a matsayi na ministocin harkokin wajen kasashen larabawa.

Wannan batu dai ya bakanta rayukan al’ummomin larabawa da na musulmi a ko’ina cikin fadin duniya.

 

 

https://iqna.ir/fa/news/3875323

 

 

captcha