IQNA

Mahmud Abbas: Trump Ba Ya Fahimtar Komai Daga Shirin Da Ya Kaddamar

22:01 - February 01, 2020
Lambar Labari: 3484474
Shugaban Falastinawa Mahmud Abbas ya caccaki Donald Trump dangane da shirinsa na yarjejeniyar karni kan Falastinu.

Kamfanin dillancin, shugaba Mahmud Abbas Abu Mazin wanda ya gabatar da jawabi dazu akan batun yarjejeniyar karni, ya bayyana cewa; Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya aike masa da kwafi na shirinsa na yarjejeniyar karni, amma ya ki karba, haka nan kuma ya kira shi ta waya, shi ma ya ki daga wayar.

Shugaban na palasdinawa ya ce ya dauki wadannan matakan ne domin ya san cewa Trump zai iya fadawa duniya cewa ya shawarce shi kafin ya kaddamar da yarjejeniyar ta karni.

Mahmud Abbas Abu Mazin ya kuma ce ko kadan bai laminta da abinda ya zo a cikin yarjejeniyar ba, domin kada tarihi ya ambace shi da cewa ya sayar da birnin kudus.

Wani sashe na jawabin shugaban na Palasdinawa ya kunshi cewa; Daga yanzu Palasdinawa ba za su laminta da Amurka ta zama ita kadai ce mai shiga tsakani ba a shirin zaman lafiya.

A yau Asabar ne aka yi taron gaggawa na kungiyar kasashen larabawa a birnin alkahira bisa bukatar Palasdinawa domin daukar mataki akan ‘yarjejeniyar karni’ da Amurka ta kaddamar da ita a ranar Talatar da ta gabata.

 

https://iqna.ir/fa/news/3875678

 

 

 

captcha