IQNA

Kungiyar Kasashen Larabawa Ta Yi Watsi Da Yarjejeniyar Karni

23:57 - February 02, 2020
Lambar Labari: 3484476
Kungiyar kasashen larabawa taki amincewa da abin da ake ira da yarjejeniyar karni kan Falastinu da Trump ya gabatar.

Kamfanin dillancin labaran IQNA, babban sakataren kungiyar kasashen larabawa ya bayyana yarjejeniyar karni wadda shugaban Amurka ya gabatar a ranar Talatar da ta gabata a matsayin wani lamari da ke sanya a yanke kauna dangane dav lamarin Amurka.

babban sakataren kungiyar kasashen larabawa ya bayyana haka ne a jiya Asabar bayan kammala taron ministocin harkokin waje na kungiyar kasashen larabawa a birnin Alkahira na kasar Masar .

Ya kara da cewa sun gudanar da taron gaggawa na kungiyar ne don nuna goyon bayansu ga falasdinawa, sannan daga yanzu sun debe kauna daga Amurkaa dangane da rikicin falasdinawa da yahudawan Isra’ila .

Ministan harkokin wajen kasar Iraqi ya bayyana cewa suna goyon bayan kafa kasar Falasdinu mai hedkwata a birnin Kudus, sannan abin da ya faru na “yarjejeniyar Karni” ya taimakawa yahudawan Isra’ila ne kawai.

 

 

 

https://iqna.ir/fa/news/3875737

captcha