Kamfanin dillancin labaran IQNA ya bayar da rahoton cewa, daruruwan mutane ne suka fito kan tituna a birnin Dalas na kasar Amurka, domin nuna rashin amincewarsu da abin da ake kira shirin Trump na yarjejeniyar karni.
masu gangamin sun hada da larabawa mazauna kasar Amurka, da kuma masu rajin kare hakkokin bil adama, awadanda suke bayyana shirin zaman lafiya da Trump ya gabatar tsakanin Isra'ila da falastinawa da cewa babu adalcia cikinsa.
Masu gangamin sun bukaci gwamnatin Amurka da ta sake yin nazari kan wannan shiri na Trump, wanda suke kallonsa matsayin wani babban abin kunya ga kasar, wanda kuma zai iya zubar da mutuncinta.