Kamfanin dillancin labaran iqna, shugabar Majalisar Wakilan Amurka Nancy Pelosi, ta kekketa takardar jawabin shugaba Donald Trump bayan ya kammala jawabinsa kan halin da kasa ke ciki a zauren majalisar kasar.
Wannan dai ya biyo bayan da Trump din, ya yi watsi da ita Pelosin a lokacin da ta mika masa hannu, wanda ake ganin hakan ne ya harzuka ta ta dau wannan matakin na walakanta shi a idon duniya.
A yayin jawabin nasa, shugaba Trump ya kauce wa batun dambarwar tsige shi.
Sai kuma wasu batutuwan da suka hada da yake-yaken Amurka a wasu kasashen duniya da shirin janye dakarun kasar daga Afghanistan.
A wannan Larabar ce ake sa ran majalisar dattawan Amurkar wadda jam'iyyar Republican ke da rinjaye a cikinta, za ta bayyana matakinta kan bukatar tsige shugaba Trump da aka gabatar mata bisa zargin yin amfani da karfin ikonsa ta hanyar da ba ta dace ba.