IQNA

Jagora: Dole Mu Zama Masu Karfi Domin Hana Aukuwar Yaki

22:55 - February 08, 2020
Lambar Labari: 3484496
Jahoran juyin juya halin muslucnia Iran ya bayyana cewa, bisa la’akari da yadda lamari ya koma yanzu dole ne Iran ta yi karfi yadda ya kamata domin a samu zaman lafiya.

Kamfanin dillancin labaran IQNA, Jagoran juyin juya halin musulunci a nan Iran Ayatullahi sayyeed Aliyul Khami’na’ii ya bayyana cewa gwamnatin “Tagud” ko sarki sha, a dai-dai lokacinda juyin juya halin musulunci ya kusan kaiwa ga nasara, an zo mata zo mata ta inda bata zata ba, a lokacinda sojojin sama na kasar suka yi bai'a wa Imam Khomaini (q).

Jagoran ya bayyana haka ne a safiyar yau Asabar a lokacinda yake ganawa da manya-manyan jami’an sojojin sama da kuma komandojinsu a gidansa, a dai-dai lokacinda ake raya ranar 19 ga watan Bahman ranar da sojojin sama na Iran suka yi bai’a ga imam Khomaini (q) a matsayin babban kwamandansu.

Jagoran ya kara da cewa wannan wata rahaman ce ta Allah ga juyin juya halin da kuma su sojojin. Kafin haka dai sojojin sama a lokacin su ne suka fi kusa da sarkin, sannan sune suka fi kusa da Amurkawa wadanda suke tare da sarkin, inji jagoran.

A rana irin ta yau ce a shekara ta 1979 sojojin sama na kasar Iran suka yi bai’a wa Imam Khomaini(q) a matsayin kwamansu a dai-dai saura yan kwanaki juyin juya halin musulunci a kasar ya kai ga nasara. Wannan ranar a nan kasar Iran, tun lokaci it ace ranar “sojojin sama na JMI”.

 

 

 

https://iqna.ir/fa/news/3877246

 

captcha