IQNA

Babban Sakatare MDD Ya Bukaci A Cire Sudan Daga Jerin Masu Taimakon Ta'addanci

23:59 - February 09, 2020
Lambar Labari: 3484503
Babban sakataren majalisar diniin duniya ya bukacia cire Sudan daga cikin jerin sunayen kasashe masu daukar nauyin ayyukan ta'addanci a duniya.

Kamfanin dillancin labaran IQNA, bababn sakataren majalisar dinkin duniya Antonio Guterres ya bayyana a wajen taron kungiyar tarayyar Afirka a birnin Addis Ababa na kasar Habasha cewa, akwai bukatar a samar da wani tsari an hadin gwiwa tsakanin Afrika da sauran kasashen duniya domin yaki da ta’addanci.

Ya ce dukaknin kasashen duniya sun yi iamni da cewa, yaki da ta’addanci aiki ne da ya rataya a kan kasashen duniya baki daya, kuma kasashen Afrika na yin aiki tare da wasu bangaroro na duniya a wannan fage.

Haka nan kuma ya Amurka da ta cire Sudan daga cikin kasashen da take lissafa sua  cikin masu mara baya ga ayyukan ta’addanci.

A cikin watan Agustan 1993 ne amurka ta saka Sudana  cikin kasashe masu daukar nauyin ta’addanci a  duniya.

Bayan kifar da gwamnatin Albashira  cikin watan Afrilun shekarar da ta gabata, sabuwar gwamnatin Sudan ta bayyana fatan ganin an cire suna Sudan daga cikin masu daukar nauyin ta’addanci.

 

https://iqna.ir/fa/news/3877468

captcha