IQNA

Jagora Ya Amince Da Yin Afuwa Ga Wani Adadi Mai Yawa Na Fursunoni A Iran

23:51 - February 10, 2020
Lambar Labari: 3484505
Jagoran juyin juya halin muslunci a Iran Ayatollah Sayyid Ali Khamenei ya amince da yin afuwa ga wasu furnoni da ke gidan kaso a kasar.

Kamfanin dillancin labaran IQNA, shafin yada labarai na jagora ya bayar da bayanin cewa, alkalin alkalan kasar Iran Hojjatol Islam Ibrahim Ra’isi, ya aike da wata wasika zuwa ga jagora da yake neman amincewarsa kan yin afuwa ga wasu daga cikin furnoni.

Bayanin ya kara da cewa jagoran ya amince da bukatar da aka gabatar masa, wadda ta kunshi yin afuwa ga wasu fursoni, wasu kuma za a sassauta hukunci a kansu, inda jimillar adadin mutane ya kai dubu biyu da 315.

A kowace shekara a lokuta daban-daban jagora ya kai yi irin wannan afuwa ga fursunoni da suka cancanci haka saboda dalilai na ‘yan adamtaka, wanda ya yi daidai da doka mai lamba 11 sakin layi na 110 da ke cikin kundin tsarin mulkin Iran.

 

 

https://iqna.ir/fa/news/3877969

captcha