IQNA

Rauhani: Juyin Iran Ya Doru Ne Kan Zabe / Sulaimani Janr Ne A Fagen Yaki Mai Diflomasiyya A Fagen Tattaunawa

23:50 - February 11, 2020
Lambar Labari: 3484510
A yayin gabatar da jawabi a gaban dimbin jama'a a yau shugaba Rauhani ya jaddada matsayin kasarsa na ci gaba da yin riko da manufofin juyi.

Kamfanin dillancin labaran IQNA, miliyoyin Mutane Sun Fito Kwasu Da Kwarkwatarsu Akan Titunan Birnin Tehran Da Sauran Garuruwan Iran Domin Raya Ranar Cin Nasarar Juyin Musulunci.

Da misalin karfe 9;00 na safiyar yau Talata ne dai al’ummar Kasar ta Iran su ka fara kwarara kan manyan tituna suna bayar da take yin tir da Amurka da HKI.

Bugu da kari, manyan jami’an gwamnati da malaman addini suna cikin masu yin Zanga-zangar ta ranar “22 ga watan Bhman’ na hijira shamshiyya da gwamnatin sarauta ta Sha ta zo karshe, shekaru 41 da su ka gabata.

Daga cikin mahalarta Zanga-zangar da akwai shugaban kasa Dr. Hassa Rauhani da ministan harkokin wajen Iran, Muhammad Jawad Zarif, da tsohon shugaban Majalisar shawarar musulunci ta Iran Natiq Nuri. Haka nan ministan limin Haji Mirzabi da wasunsu.

A wani sashe na Zanga-zangar, an rataye mutum-mutumin shugaban kasar Amurka Donald, a mastayin hukunta shi bisa laifin ta’addanci na kashe shahid Kassim Sulaimani.

A cikin kusan dukkanin manyan biranen Iran da kauyuka ana gudanar da wannan irin Zanga-zangar a yau.

A karshe masu Zanga-zangar kan fitar da bayani da yake kunshe da muhimman matakan da za a dauka akan makiya.

 

 

https://iqna.ir/fa/news/3878098

captcha