IQNA

Gasar Kur’ani Ta Kasa Da Kasa A Masar A Daidai Lokacin Da Ake Tsoron Yaduwar Corona

23:50 - March 01, 2020
Lambar Labari: 3484574
Tehran (IQNA) mahkunta a kasar Maar sun sanar da cewa duk da barazanar yaduwar cutar corona a duniya za a gudanar da gasar kur’ani ta duniya a kasar.

Shafin yada labarai na Yaum Sabi ya bayar da rahoto ewa, Adel Gadban gwamnan lardin Port Said na kasar Masar ya bayyana cewa, an kammala dukkanin shirye-shirye na gudanar da gasar kur’ani ta duniya a wannan lardi, tare da halartar kasashe 40 na duniya.

Ya ce babban abin alfahari gare su kan yadda wannan gasa take gudana a karo na uku kenan a cikin lardin Port Sa’id, inda ya ce a shekarar bana ma da yardarm Allah gasar za ta fara gudana a karshen wannan mako.

Gasar dai tana samun halartar manyan jami’an gwamnati da kuam malamai daban-daban daga sassa na kasar ta Masar, gami da wakilan kasashen duniya.

Khaled Mujahid kakakin ma;aikatar kiwon lafiya na kasar Masar yak ore labarin da ke cewa akwai mutane 6 a kasar ad suke dauke ad cutar corona.

Ma’aikatr kiwon lafiya ta Masar ta bayyana cewa, mutum daya ne aka samu da cutar a kwanakin baya, kuma  ahalin yanzu ya warke tangaram babu kwayoyin cutar tare da shi.

 

3882239

 

 

 

 

captcha