A zanatawarsa da kamfanin dillancin labaran iqna, Samih Ahmad Khaled Usmanah ya bayyana cewa, Sheikh Barakat ya rasu a yau bayan fama da rashin lafiya na tsawon lokaci.
Ya bayyana rasuwar sheikh Barakat da cewa babban rashi ne ga dukkanin musulmi, musamman ma ma’abota kur’ani mai tsarki.
An haifi Sheikh Barakat a kasar Lebanon a cikin shekara ta 1971, kuma ya sam shedar kammala karatu daga jami’ar Azahar ta kasar Masar, kamar yadda kuma ya kasance daya daga cikin fitattun makaranta kur’ani na kasa da kasa.
Baya ga haka kuma shi ne babban limamin Juma’a na birnin Tarabulus birni na biyu mafi girma akasar Lebanon, kamar yadd kuma yana daga cikin malamai a bangaren addini a jami’ar birnin Beirut.
Yana daga cikin manyan alkalan gasar kur’ani ta duniya, kuma ya halarci taruka daman a addinin muslunci a kasashen duniya daban-daban.