IQNA

Babbar Jami’ar Malaysia Ta Yanke Alaka Da Kamfanin PIMA Saboda Taimaka Ma Isra’ila

23:58 - March 01, 2020
Lambar Labari: 3484576
Tehran (IQNA) babbar jami’ar kasar Malaysia ta yanke alaka da kamfanin PIMA saboda taimaka ma gwamnatin yahudawan Isra’ila da yake yi.

Shafin yada labarai na kwamitin kamfen kaurace wa  sayen kayan Isra'ila na BDS ya sanar da cewa, babbar jami'ar kasar Malaysia ta UiTM ta yanke alaka da kamfanin PUMA, saboda taimaka ma gwamnatin yahudawan Isra'ila da kamfanin ke yi.

Bayanin ya ce jami'ar ta kulla wata yarjejeniya tare da kamfanin domin samar da kayan wasanni ga babbar kungiyar kwallon kafa ta wanann jami'a har tsawon shekaru uku, amma a halin yanzu sakamakon yadda kamfanin ya haarci wani taron yahudawa na taimaka ma Isra'ila a kasar Jamus, jami'ar ta yanke alaka da wannan kamfani baki daya.

A kwanaki baya ne dai majalisar dinkin duniya ta saka kamfanonin da suke da alaka da ayyukan gina matsugunnan yahudawa a cikin yankunan Falastinawa, a cikin jerin kamfanonin da ayyukansu ba su da halasci, daga ciki kuwa har da kamfanin «Delta Galil» da yake wa PUMA aiki.

Kungiyar BDS tana gudanar da aikace-aikacenta ne na fadakar da al'ummomin duniya irin zaluncin da yahudawan sahyuniya suke yi wa al'ummar Falastinu, da kuma yadda duniya take yin biris kan abin da yake faruwa a Falastinu, tare da yin kamfe na a kaurace wa kayan da Isra'ila take samarwa.

 

 

3882365

 

Abubuwan Da Ya Shafa: malaysia kamfanin PIMA yahudawa
captcha