IQNA

Hukumar Lafiya Ta Duniya Ta Aike Da Kayan Yaki Da Cutar Corona Zuwa Iran

23:53 - March 02, 2020
Lambar Labari: 3484579
Tehran (IQNA) Hukumar lafiya ta duniya ta aike da kayayyakin aiki zuwa kasar Iran domin yaki da cutar coronavirus a kasar.

Jaridar Quds Alarabi ta bayar da rahoton cewa, a karon farko hukumar lafiya ta duniya ta aike da kayan aiki zuwa kasar Iran domin yaki da cutar corona a yau Litinin.

Bisa ga wannan rahoto, hukumar ta yi amfani da jiragen kasar UAE ne wajen daukar kayayyakin daga Dubai zuwa cikin kasar ta Iran, kayan kuwa sun hada da ababen rufe fuska da kuma kayan gwaji da sauransu.

Robert Blanchard daya daga cikin jami'an hukumar lafiya ta duniya ya bayyana cewa, kayan da suka tura Iran sun kai kimain ton 7.5, wanda kudinsu ya kai kimanin dala dubu 300.

Ya kara da cewa, daga cikin kayayyakin baya ga abubuwan rufe fuska da kuma safar hannu mai dauke da maganin kariya, akwai kayan aikin tiyata da kuma na'urori masu taimakawa wajen lumfashi.

A nasu bangaren kasashen Jamus, Faransa da Burtaniya sun sanar da shirinsu na kai dauki ga kasar Iran, wanda kayayyakin da za su za su kai na kimanin yuro miliyan biyar.

Ali Reza Ra'isi mataimakin minstan lafiya na Iran ya bayyana cewa, adadin wadanda suka kamu da cutar ya kai 1501 a kasar, yayin da wadanda suka rasu adadinsu ya kai 66 ya zuwa yanzu.

 

3882773

 

captcha