IQNA

An Sake Bude Masallacin Harami Da Masallacin Manzo (SAW) A Madina

23:55 - March 06, 2020
Lambar Labari: 3484591
Tehran (IQNA) an sake bude masallacin haramin Makka mai alfarma da masallacin manzon Allah (SAW) a Madina.

Tashar Sky News Arabi ta bayar da rahoton cewa, bayan gudanar da feshin magungunan kamuwa da cutar corona, a yau an sake bude masallacin haramin Makka mai alfarma da masalacin manzon Allah (SAW) a Madina ga masu ziyara.

Kafin wannan lokacin dai mahkuntan kasar Saudiyya sun sanar da hana bayar da visa ga masu ziyara daga kasashe 25 saboda tsoron yaduwar corona.

Wata majiya ta tabbatar da cewa, masallacin harami da masallacin manzon Allah (SAW) a Madina, za su zama bude ne a kowace rana har zuwa sa’a daya bayan sallar Isha’i, daga nan za  arufe su har sa’a daya kafin sallar asubahi.

A cikin bayanin da mahukuntan Saudiyya suka bayar kan adadin mutanen da aka tabbatar da cewa sun kamu da corona a kasar, ya zuwa yau ya kai mutane biyar.

3883506

 

 

 

 

 

captcha