IQNA

Tawagar Hamas Ta Gana Da Jakadan Iran A Moscow

23:56 - March 06, 2020
Lambar Labari: 3484592
Tehran (IQNA) Tawagar kungiyar Hamas karkashin jagorancin Isma’il Haniyya ta gana da jakadan kasar Iran a birnin Moscow na kasar Rasha.

Rahoton ya Ambato cewa, tawagar Hamas wadda ke gudanar da ziyara a kasar Rasha, karkashin jagorancin Isma’il Haniyya ta gana da jakadan kasar Iran a birnin Moscow Kazem Jalali.

Bangarorin biyu sun tattauna kan muhimman batutuwa da suka shafi halin da ake ci a yankin gabas ta tsakiya, da kuma batun shirin Trump da ake kira da yarjejeniyar karni.

Jakadan Iran a Rasha ya bayyana cewa, dole ne kasashen msuulmi su dauki mataki na bai daya domin tunkarar wanann shiri da ke nufin wargaza batun Falastinu da makomar al’ummarta, da sunan yarjejeniyar zaman lafiya.

Shi ma a nasa bangaren jagoran kungiyar Hamas Isma’il Haniyya ya bayyana cewa, batun shirin yarjejeniyar karni batu ne da yake tatatre da munafunci da mairci, wanda Aurka da Isra’ila da kuma kawayensu suka shirya a kan al’ummar Falastinu, wanda kuma tuni falastinawa suka yi watsi da shi.

Haka nan kuma Haniyya ya bayyana cewa, suna goyon irin matakin da kasar Iran take dauka na kin amincewa da wanann shiri, da kuma dagewa kan mara baya ga al’ummar Falastinu.

 

 

3883485

 

 

 

 

captcha