IQNA

An Bukaci A Kare Hakkokin Mata Musulmi A Kasar Canada

23:55 - March 08, 2020
Lambar Labari: 3484599
Tehran (IQNA) wata cibiyar mata musulmi a kasar Canada ta yi kira da a kare hakkokin mata musulmi masu saka hijabi a kasar.

Shafin yada labarai na about Islam ya bayar da rahoton cewa, wata cibiyar mata musulmi a birnin Montrial na kasar Canada ta yi kira da a kare hakkokin mata musulmi masu saka hijabi a kasar a ranar mata ta duniya.

Ya zo a cikin bayanin kungiyar cewa, tun bayan da majalisar dokokin jihar Cubec ta kafa dokar hana mata musulmi saka hijabia  wasu wuraren ayyuka, tun daga lokaci mata musulmi da suka kammala karatu a jami’oi suna fusakantar matsala wajen samun aikin yi.

A cikin shekara ta 2019 ce majalisar jihar Cubec ta kafa dokar haramta wa mata msuulmi saka hijabi a makarantun gwamnati, da lauyoyi da kuma alkalai gami da ‘yan sanda.

Haka nan kuma bayanin ya kara da cewa, wani abu mafi muni da ya faru ma shi ne, bayan kafa wannan doka kyamar mausulmi mata masu saka hijabi ta karu fiye da kowane lokaci a baya a kasar.

 

 

3883884

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: canada hakkokin mata musulmi hijabi makarantu
captcha