Kamfanin dillancin labaran Saumaria News ya bayar da rahoton cewa, Ayatollah Sheikh Jawad Alkhalisi daya daga cikin manyan malaman addini a kasar Iraki ya bukaci a kori jakadun Amurka da Burtaniya daga kasar saboda yada barna da munanan dabiu da suke a tsakanin al’ummar kasar.
Ya ce hakika ofisoshin jakadanci na kasashen Amurka da da Burtaniya da suke a cikin kasar Iraki, suna yada barna a tsakanin alumma musamman ma matasa, inda suke karkatar da su daga koyarwa irin ta addini, wanda hakan ya saba wa dukkanin ka’idodi da yarjejeniyoyi da huldar diflomasiyya.
Malamin ya ce yana yin kira ga mahukunta da su sauke nauyin da ya rataya a kansu na kubutar da Iraki ta hanyar korarar jakadun wadannan kasashe biyu.