IQNA

Yarjejeniyar Amurka Da Taliban Ta Samu Goyon Bayan Kwamitin Tsaro

22:47 - March 11, 2020
Lambar Labari: 3484612
Tehran (IQNA) Jami'in Amurka kan harkokin ya bayyana cewa kwamitin tsaron majalisar dinkin duniya ya amince da aka cimmawa tsakanin Taliban da Amurka.

Jami'in ya bayyana a cikin shafinsa na twitter cewa, mambobin kwamitin tsaro sun amince da taftarin kudirin da aka gabatar musu kan tattaunawar Amurka da Taliban, da ke neman dakatar da bude wuta a kasar Afghanistan.

Ya ce babbar manufar hakan ita ce samo hanyoyin da za su kawo karshen yaki da tashe-tashen hankula  akasar Afghanistan, wanda kuma aiwatar da abubuwan da yarjejeniyar ta kunsa daga dukkanin bangarorin biyu zai iya haifar da da mai ido ga makomar kasar.

Haka nan kuma ya bayyana cewa, abu na gaba da yake da muhimamnci a yanzu bayan cimma wannan yarjejeniyar, shi ne mayar da bangarorin gwamnati da Taliban kan teburin tattaunawa, domin samun sulhu da fahimtar juna  a tsakaninsu, da hakan zai kawo wanzuwar zaman lafiya mai dorewa  a kasar Afghansitan.

Tuna  cikin shekara ta 2001 ce dai Amurka ta kaddamar da hare-harea  kasar Afghanistan da sunan kifar da gwamnatin Taliban, wanda kuma tun daga lokacin har zuwa yanzu kasar ba sake sheda zaman lafiya ba.

3884561

 

 

captcha