IQNA

An Dakatar Da Sallar Juma’a A Babban Masallacin Brussels

23:56 - March 12, 2020
Lambar Labari: 3484615
Tehran (IQNA) an sanar da dakatar da sallar Juma’a a babban masallacin birnin Brussels na kasar Belgium sakamakon yaduwar cutar corona.

Kamfanin dillancin labaran KUNA ya bayar da rahoton cewa, kwamitin babban masallacin masallacin birnin Brussels na kasar Belgium, ya sanar da dakatar da sallar Juma’a sakamakon yaduwar cutar corona a kasar.

Bayanin ya ce daukar wannan mataki ya zo ne sakamakon yadda ake samun yaduwar cutar a tsakanin mutanen kasar cikin sauri, wanda hakan zai iya shafar mutane da suke taruwa a cikin masallaci.

Haka nan kuma kwamitin masallacin ya sanar da cewa, an fara gudanar da aikin feshen maganain kwayoyin cuta  acikin masallacin da kewaye.

A jiya Laraba gwamnatin Belgium ta sanar da cewa mutane 47 sun kamu da cutar corona, wanda hakan ya daga adadin mutanen da suka kamu da cutara  kasar zuwa 314 ya zuwa yanzu.

3884886

 

 

captcha