IQNA

An Kafa Kwamitin Bincike Kan Harin Amurka A Karbala

0:07 - March 19, 2020
Lambar Labari: 3484635
Tehran (IQNA) an kafa wani kwamiti domin gudanar da bincike kan irin makaman da Amurka ta yi amfani da su wajen kai hari a Karbala.

Ministan kiwon lafiya da kula da muhalli na kasar Iraki ya kafa wani kwamiti domin gudanar da bincike kan irin makaman da Amurka ta yi amfani da su wajen kai hari a filin sauka da tashin jiragen sama a Karbala a makon da ya gabata.

Wannan bincike dai yana zuwa ne a daidai lokacin da ake zargin Amurka da yin amfani da wasu sanadari masu guba wajen kai harin a filin sauka da tashin jiragen sama na Karbala, wanda a halin yanzu ana cikin gina shi ne.

Salam Khudair babban daraktan cibiyar gwaje-gwajen sanadarai ta kasa a Iraki ya bayyana cewa, suna gudanar da bincike kan wannan batu, kuma da zaran sun kammala za su sanar da sakamakon binciken nasu.

Amurka ta kai wa filin jirgi na Karbala hari ne bisa hujjar cewa tana mayar da martani, kan harin da aka kai kan sansanin sojojinta da ke yankin Taji a cikin makon da ya gabata.

 

3886413

 

 

 

 

captcha