IQNA

Jagora Ya Sanya Wa Shekarar 1399 Hijira Shamsiyya Sunan Shekarar Habbaka Sana’oin Cikin Gida

15:02 - March 20, 2020
Lambar Labari: 3484638
Tehran (IQNA) Ayatollah Khamenei jagoran juyin juya halin musulunci a Iran, a lokacin da yake gabatar da jawabi akan sabuwar shekarar Norouz ta hijira Shamsiyya, ya fara taya al’ummar alhinin zagayowar lokacin Shahadar Imam Musa Bin Jaafar Kazem (AS) da kuma murnar Mab’as, da kuma jajantawa al’umma matsaloli na annoba da aka shiga.

Shafin jagora ya ambata cewa, a cikin jawabinsa na sabuwar shekara hijira shamsiyya ta 1399, jagoran juyin juya halin muslunci Ayatollah Sayyid Ali Khamaenie ya fara ne da isar da sakon ta’aziyya ga dukkanin al’umma kan zagayowar lokacin shahadar Imam Musa Bin jaafar Kazem (AS) kamar yadda kuma ya mika sakon taya murna ga dukkanin al’ummar musulmi, kan zagayowar lokacin aiko ma’aki tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi.

Baya ga haka kuma ya mika sako na jinjina ga iyalan dukkanin wadanda suka yi shahada wajen kare juyin juya halin muslunci a kasar. Inda ya bayyana shekarar da ta gabata ta 1398 dacewa shekara ce da dukkanin al’ummar kasar Iran suka rashi na babban gwarzo jarumi, wanda ya sadaukar ransa domin kare martabar addinin muslunci janar Wasem Soleimani, wanda kuma makiya addinin Allah makiya al’umma ne suka kashe shi.

Haka nan kuma yayin da yake yin ishara da wasu lamurra da suka faru na bakin ciki a kasar, jagoran bayyana abin da ya faru a Keraman da kuma hatsarin jirgin da ya faru bisa kure, da jami’an kiwon lafiya da suka rasa rayukansu a  lokacin gudanar da ayyukansu na taimakon jama’a, da kuma dukkanin wadanad suka rasu sakamakon cuta ta annobar corona, dukkaninsu suna a matsayin abin girmamawa ga al’ummar kasa baki daya.

Ya ce hakika shekarar da ta gabata shekara wadda take cike da abubuwa na takaici da tsanani ga al’ummar Iran a ta bangarori da dama, sakamkon dalilai da dama, amma kuma bayan tsanani akwai sauki a tafe da yardar Allah madaukakin sarki.

Shekaru da kuma ranakun rayuwar dan'adam cike suke da dama da kuma barazana da kalubale. A saboda haka wajibi ne mu zamanto masu amfanuwa da damar da muka samu, sannan mu kuma mayar da barazanar da muke fuskanta zuwa ga wata dama.

Ya kara da cewa daga cikin abubuwa wadanda suke faranta raia  shekarar da ta gabata, har da yadda mutane suka sadaukantar da kansu wajen taimakon mutanen da ambaliyar ruwa ta shafa a wasu sassa na kasar, da kuma yadda miliyoyin jama'a suka fito wajen janazar janar Qasem Soleimani a Tehran, Qom, Isfahan, Ahwaz da kuam Mashhad.

Haka nan kuma a bangaren matsalar corona, jama'a sun taka rawar gani, musamman jami'ai a bangaren kiwon lafiya, da kuma dalibai a jami'io a wannan bangare, inda suka sadaukar kansu da lokutansu domin hidima ga jama'a, da kuma taimaka ma wadanda suka kamu da wannan cuta.

Ya kara da cewa, dangane da sauran al'umma kuwa, ya zama wajibi dukkanin mutane su bayar da hadin kai ga jami'an kiwon lafiya, tare da aiwatar da abin da suka uamrta, da kuma kaucewa abin da suka yi umarni da a kiyaye shi.

Jagoran ya ce babu wata al'umma da za ta iya samun abin da take bukata cikin sauki, amma duk da irin matsaancin halin da aka saka al'ummar Iran a ciki, suna yin iyakacin kokarinsu a dukkanin bangarori, kamar yadda kuma da yardar Allah za su yi galaba a kan matsalar ad suke ciki a halin yanzu.

A lokacin da yake kira ga mutane kan kara yin tsayin daka wajen fuskantar yanayin da suke ciki da karfin imani kuwa, ya bayyana cewa a duk lokacin da mumini ya shiga cikin wani matsi ko kunci, fuskantar lamarin da karfin imani da dogaro da Allah shi ne babbar mafita.

Ya ce bisa la'akari da matsanancin halin da aka saka al'ummar Iranta hanyar saka musu takunkumai da sauran hanyoyi na matsin lamba, wannan ya shafi rayuwar jama'a ne kai tsaye ta fuskokin rayuwa da sauransu, wanda kuma ci gaba da kara bunkasa ayyukan sana'oi na cikin gida a dukkanin bangarori, shi ne hanyar karya lagon makiya ta wannan fuska.

Ya yi ishara da cewa,a  duk lokacin da ake son tunkari matsala irin wannan, to dole ne sai gwamnati ta kara rubanya dukkanin kokarinta da tallafinta a dukkanin bangarori, ta yadda jama'ar kasa za su ci moriyar gudunmawar da gwamnati take bayarwa wajen inganta rayuwarsu, kama daga bangaren kyautata ayyuka na bankuna, da kamfanoni da kasuwanni, da saka kudade domin ragen kimar kaya, ta yadda kowane dan kasa zai iya sayen duk abin yake bukata cikin sauki da rahusa.

Ya ce a kan haka ne ma aka saka wa wananns hekara sunan shekarar habbaka sana'oin  cikin gida, domin hakan ne babban abin da zai sanya makiya su yanke kauna,a  lokacin da suka ga al'umma ta dogara da kanta wajen samar da abubuwan da take bukata na rayuwa.

Ya kara da cewa wannan ba aiki ne da ya takaita a kan gwamnati ita kadai ba, dukkanin sauran bangarori ba dole ne su sanya hannu, domin hakan shi ne zai sanya aiki ya zama na al'umma baki daya.

Daga karshe ya kara taya al'ummar musulmi murnar zagayowar lokacin aiko ma'aiki tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da alayensa tsarkaka.

 

 

3886557

 

captcha