IQNA

Kungiyoyin Musulmi A Kasar Malaysia Sun Yi Allawadai Da Takunkumin Amurka kan Iran

23:57 - March 23, 2020
Lambar Labari: 3484650
Tehran (IQNA) gamayyar kungiyoyin musulmi a kasar Malaysia sun yi Allawadi da kakkausr mury kan takunkuman Amurka a kan Iran.

A cikin bayanin hadin gwiwa da suka fitar, kungiyoyin musulmi a kasar Malaysia sun bayyana takunkumin Amurka a kan kan Iran da cewa abin Allawadai, domin kuwa yana kawo cikas ga kokarin yaki da cutar corona a kasar.

Bayanin ya ce da babu takunkumin Amurka a kan Iran, da kasar ta yi fiye da abin da ta yi a halin yanzu ta fuskar yaki da corona, da adadin mutane da suka mutu ko suka kamu ba su yadda suka kai ba  a halin yanzu.

A daya bangaren kuma gamayyar kungiyoyin muuslmi na kasar Malaysia sun bukaci kasashen duniya da su yi watsi da takunkumin na Amurka a kan Iran, domin ci gaba da taimaka mata wajen yaki da wannan cuta.

A cikin ‘yan kwanakin da suka gabata ma kasashen duniya da dama da suka hada da Rasha da kuma Sin, duk sun yi Allawadai da wannan mataki na Amurka, tare da yin kira ga Amurka da ta kawo karshen wannan takunkumin na siyasa a kan Iran.

 

 

3887042

 

 

 

captcha