Jaridar Tribune ta kasar Pakistan ta bayar da rahoton cewa, shugaban kasar Pakistan Arif Alawi ne ya bukaci wannan fatawa daga cibiyar ta Azhar.
Ya zo a cikin wannan fatawa cewa, bisa la’akari da cewa taruwar mutane a wuri guda na iya jawo yaduwar cutar corona, saboda haka ya halasta a dakatar da sallolin jam’i da kuma sallolin Juma’a.
Fatawar ta ce ya zama wajibi a kan gwamnatocin kasashen musulmi da su dauki matakai, daga cikin har da hana sallolin jam’i, domin kaucewa yaduwar annobar a tsakanin al’umma.
Ya zuwa yanzu mutane kimanin dubu 450 ne aka tabbatar da sun kamu da cutar corona a duniya, yayin da fiye da dubu 19 da 800 daga cikinsu suka rasa rayukansu.