IQNA

An Yaba Wa Musulmi Jamus Kan Kokarinsu A Fagen yaki Da Corona

22:59 - March 28, 2020
1
Lambar Labari: 3484665
Tehran (IQNA) a Jamus an yaba da irin gagarumar gudunmawar da malaman musumi suke bayarwa wajen dakile yaduwar corona a duniya.

Kamfanin dilalncin labaran Iqna ya habarta cewa, tashar talabijin ta DW mallakin gwamnatin Jamus ta bayar da rahoton cewa, a irin gudunmawar da malaman addinin muslunci suka bayar wajen dakile yaduwar corona a kasashensu da ma kashen duniya babban abin jinjina ne.

A cikin rahoton da tashar ta bayar ta ce malamai da jagororin musulmi suna yi fadakar da mabiyansu kan wajabcin kiyaye abubuwan da jami’an kiwon lafiya suke yin kira da ake kiyaye domin kaucewa kamuwa ko yada cutar corona, daga ciki har da haduwar jama’a da yawa a wuri guda.

A kasar Iraki babban malamin addini na kasar Ayatollah Sayyid Ali Sistani ya fitar da fatawa kan hakan, inda kuma miliyoyin jama’a masu binsa a kasar da ma wasu kasashen duniya suke yin aiki da fatawar tasa.

Haka lamarin yake a kasar Turkiya, inda shugaban cibiyar addinai ta kasar Ali Arbash ya fitar da bayani makamancin wannan.

Rahoton ya cea kasashen duniya da dama malaman musulmi suna bayar da gudunmawa wajen fadakar da mabiyansu kan hanyoyin da suka dace a bi wajen kare kai daga cutar ta corona, wanda hakan yana da babban tasiri a cikin jama’a musamman ma musulmi.

 

3887794

 

Wanda Aka Watsa: 1
Ana Cikin Dubawa: 0
Ba A Iya Watsa Shi: 0
Naziru yahuza
0
0
Allah y kadawa musulinci daukaka aduniya da zamun nasar aduk inda musulmi y ke Allah y kiyayezhi gaba da baya Allah y karawa annabi daraja
captcha